A ranar 26 ga watan Oktoban da ya gabata, hukumomin kasar Sin sun fitar da sabbin matakai don kara tallafawa kamfanoni masu zaman kansu, za a kara kaimi wajen rage kudaden da kamfanoni masu zaman kansu suke kashewa, da karfafa goyon bayan kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, da inganta samar da filaye.